Rasha: An tsare dubban magoya bayan Navalny
January 23, 2021Talla
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka wallafa faya-fayen da ke nuna yadda jami'an tsaron da suke rufe fuskokinsu tare da cin zarafin masu zanga-zangar.
Daruruwan mutane ne dai suka taru a tsakiyar birnin Moscow don gudanar da zanga-zanga, sai dai kuma hayaki mai sa hawaye da 'yan sanda suka harba ya haifar da arangama a tsakaninsu da masu zanga-zangar.
Sai dai kuma wani na hannun daman madugun adawar da ke a tsare a yanzu Leonid Volkov ya ce 'yan adawa za su ci-gaba da gudanar da zanga-zangar a karshen mako mai zuwa don neman a saki Navalny.
Mutane fiye da 2000 ne aka kama a ranar Asabar yayin zanga-zanga a sassan kasar ta Rasha wadanda ke nuna goyon baya ga madugun adawar Alexei Navalny.