1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na nazarin mayar da martani kan Amirka

Salissou Boukari
December 30, 2016

Maikatar harkokin wajen kasar Rasha ta gabatar da sunayen wasu jami'an diflomasiyyar kasar Amirka guda 35 a matsayin wadanda ya kamata a kora daga kasar don maida martani. Sai dai Shugaba Putin ya ce a dakata.

https://p.dw.com/p/2V3kc
China Treffen Putin Obama
Hoto: picture-alliance/Sputnik/A. Druzhinin

Jami'ai 31 da aka bayar da sunayensu na aiki a ofishin jakadancin Amirka a Moscow, sannan da wasu jami'ai guda hudu su kuma da ke aiki a karamin ofishin jakadancin kasar Amirka a birnin Petersburg da ke Arewa maso yammacin kasar, inda aka mika sunayensu ga shugaban kasa Vladimir Putin a matsayin wadanda za a kora a wani mataki na mayar da martani ga matakin da Amirka ta dauka na korar wasu jami'an diflomasiyyar kasar ta Rasha guda 35 bisa zargin kasar ta Rasha da shishigi a harkokin zaben kasar ta Amirka da ya gudana.

Sai dai kuma duk da haka, Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya ce Rasha ba za ta kori kowa ba, har sai ta ga matakin da sabuwar gwamnatin da za ta kama aiki ta Donald Trump za ta dauka a nan gaba kan huldarta da kasar ta Rasha.