SiyasaTurai
Rasha ta bukaci Ukraine ta mika wuya don samun zaman lafiya
June 14, 2024Talla
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci Ukraine da ta mika wuya ga Moscow, idan har tana son ganin an bude kofar tattaunawar da za kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Karin bayani:Ukraine ta kai farmaki kan jirgin yakin Rasha mafi girma
Mr Putin ya yi wannan kira ne a Juma'ar nan, lokacin da ake shirin fara taro na musamman a Switzerland, kan hanyoyin bi don samar da zaman lafiya a Ukraine, wanda tuni ma shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya isa kasar.
Karin bayani:NATO: Tattauna karin makamai ga Ukraine
To sai dai wannan kira na Moscow bai samu karbuwa ba daga Kyiv, bayan da ta bukaci Rasha ta janye dakarunta baki-daya daga yankunanta da ta mamaye, ciki har da Crimea, idan har da gaske take tana son a sulhunta.