1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun dubi rikicin Mali da Zambiya a Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe M. Ahiwa
July 8, 2022

Kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika ta katse takunkumin da aka kakaba wa Mali watanni shida baya sakamakon jan kafa wajen shirya zabe. Wasu jaridun Jamus sun dubi wannan.

https://p.dw.com/p/4Ds73
Afrika ECOWAS Gipfel
Hoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Jaridar die tageszeitung ta ce takunkumin ya haifar da kishin kasa fiye da shekarun baya a Mali, lamarin da ya kai ga rungumar Rasha hannu biyu tare da juya wa yammacin duniya baya. An dakatar da aikin sojojin rundunar hadin gwiwar Faransa da kasashen Turai, sannan gwamnatin kasar Mali ta sanar cewa ba za ta bari rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA ta sauya aikinta na kare rayukan talakawanta ba.

die tageszeitung ta bayyana cewa ba a warware dukkan matsalolin da ke tsakanin Mali da ECOWAS ko CEDEAO ba. Shugabannin na yammacin Afirka sun dage kai da fata cewa bai kamata sojojin da ke mulki su samu damar tsayawa takara a zabe mai zuwa ba. Sai dai wata sabuwar dokar zabe da shugaban mulkin sojan Mali Assimi Goita ya sa wa hannu a ranar 24 ga watan Yuni, ta ba da damar takara ga sojoji bisa sharadin yin murabus akalla watanni shida kafin zabe.

Ta ce akwai bukatar "Majalisar rikon kwarya ta kasa" wadda sojoji suka kafa ta sake rubuta daftarin dokar zabe da gwamnatin Firayiminista Choguel Maiga ta kafa. Idan kuwa hakan bai samu ba, ba makawa za a ci gaba da rikici tsakanin Mali da makwabtanta da kuma tsakanin sojojin Mali da 'yan farar hula da 'yan adawa na kasar.

Afrika ECOWAS Gipfel
SHugabannin ECOWAS lokacin taro kan MaliHoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Ita kuwa Neue Zürcher Zeitung ta mayar da hankali ne kan tasirin yakin Rasha da Ukraine a Afirka, inda ta ce Rasha na cin nasara a yakin bayanai, sakamakon bacin rai game da manufofin yammacin duniya a yammacin Afirka. Jaridar ta ce rikici tsakanin Rasha da kasashen Yamma na yaduwa a Afirka a matsayin yakin bayanai musamman ma a yankin Sahel, inda ake fuskantar kalubalen tsaro.

'Yan ta'adda na yaduwa a kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, lamarin da ya kai ga kashe dubban fararen hula yayin da miliyoyin da suka yi gudun hijira. Sojojin Faransa sun shafe shekaru 10 a yankin ba tare da iya yi komai ga maharan ba. Sai dai sojojin haya na Wagner na Rasha sun maye gurbin sojojin Faransa a Mali. Sai dai bisa ga ra'ayoyin da 'yan yankin na yammacin Afirka ke yadawa a kafofinsada zumunta, abu ne mai sauki na gane cewa sun fi kusanci da Rasha.

A nata bangaren Frankfurter Allgemeine Zeitung ta wallafa sharhi mai taken bashi ya zo wa Zambiya iya wuya. Jaridar ta ce kasar ta gabashin Afirka na iya zama misali a fannin samun nasarar yafe bashin da ake binta - idan China ta kakkabe hannayenta daga tattalin arzikin Zambiya. A ziyarar da ta kai a baya-bayan nan a birnin Lusaka, Samantha Powers shugabar hukumar ci gaban kasashe na Amirka ta US AID, ta bayyana cewa Zambia na daya daga cikin kasashen da ke neman bin tafarkin dimokuradiyya a Afirka.