Rikicin Siriya zai shafi kasashe makwabta
December 10, 2024Babu shakka kifewar gwamnatin Bashar Assad ta Siriya za ta sauya dangantakar kasar da makwabtanta. Kungiyar 'yan tawayen HTS a takaice wato Hayat Tahrir al-Sham ta yi nasarar kawo karshen gwamnatin ta Assad bayan shekaru biyar da kungiyar ta kwashe tana rike da yankin arewa maso yammacin birnin Idlib. Sai dai a yanzu da ta yi nasarar kwace mulkin kasar, masharhanta na kokonta ko kungiyar na da karfin da za ta iya mulkar kasar gaba daya domin akwai wasu kungiyoyin 'yan tawaye irin HTS da ke a Siriyan da su ma za su bukaci dandana mulkin da suka jima suna hankoron kwata. Wannan fargabar ce kuma ta sanya fantsamar 'yan gudun hijira musamman daga yankin na Idlib, a cewar David Carden, mataimakin babban jami'in kula da ayyukan agaji na Majalisar Dinkin Dduniya.
Karin Bayani: Martani kan kifar da gwamnatin Siriya
Shekaru da dama da suka gabata Siriya karkashin jagorancin Bashar al-Assad ta dauki kasashen Rasha da Iran da kungiyar 'yan tawaye ta Hezbollah ta Lebanon a matsayin abokan huldarta a ketare. Kungiyar kasashen Larabawa 22 ta Arab league ta dawo da mu'amulla da Siriyan a shekarar da ta gabata bayna kwashe shekaru 12 da kungiyar ta janye jikinta da Siriya saboda tabargazar shugabanci da ta zargi Assad da aikata wa a yakin basasar kasar. Yanzu da gwamnatin Assad din ta ruguje, makwabtan Siriya irinsu Lebanon da Jordan da Iraki da Isra'ila duk sun tsaurara tsaro a kan iyakokinsu domin dakile duk wata barazanar tsaro, a cewar Nanar Hawach, babban manazarci a kungiyar International Crisis Group da ke nazarin rikice-rikice a duniya. Jami'in ya ce Isra'ila ta yi maraba da faduwar gwmanatin Bashar Assad domin ya kasance aminin Iran da kungiyar mayakan Hezbollah da ba sa ga maciji da Isra'ila.
Shugabancin kungiyar HTS da ta karbe iko da Siriya ya ce ba za su takura wa mata rufe jikinsu ko kuma dakile wa jama'an Siriya 'yancinsu a fannoni dabam-dabam, amma masu sharhi na cewa akwai gagarumin aiki gaban sabbin jagororin Siriya na sauya akalar kasar yadda za su samu amincewar kasashen duniya irin Turkiyya da kungiyar Tarayyar Turai da kuma Amurka.