Mali ta shiga cikin rikicin siyasa
July 16, 2020Tun daga karshen makon da ya gabata ne dai, kasar Mali da ke fama da hare-hare daga 'yan ta'adda masu da'awar jihadi da rikicin kabilanci, ta tsinci kanta tsundum cikin sabon rikicin siyasa da ya barke. Wata kungiya ta hadakar jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula karkashin jagorancin wani jagoran addinin Imam Mahmoud Dicko da ake yi wa lakabi da M5 ke jagorantar zanga-zangar da ke neman jefa kasar ta Mali cikin wani wadi na tsaka mai wuya.
Masu zanga-zangar dai saun bukaci da a rushe majalisar dokokin kasar da kotun tsarin mulki, kana shi ma Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta bai tsira ba, domin kuwa masu zanga-zangar sun ce tilas shi ma ya sauka daga kan karagar mulki.
Sai dai a yanzu kura ta lafa, inda a nata bangaren gwamnati ta dauki matakin sako wasu masu zanga-zangar da jagororin 'yan adawa da ta kama. A hannu guda kuma tuni kungiyar habaka tattalin arzikin yankin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko kuma CEDEAO, ta dauki matakin tura wata tawaga karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan domin yayyafawa wutar rikicin ruwa.