Alamun rudani a fagen siyasar Najeriya
October 18, 2022A wani abun da ke zama alamun rikicin da ake shirin gani a cikin fagen siyasar Najeriya, ana dada fuskantar tashin hankali a dandalin yakin neman zaben da ke gudana a cikin kasar a halin yanzu. An dai kai har ya zuwa alkawari a tsakanin manyan jam'iyyun kasar dama na kanana bisa zama na lafiya a yayin zabe. To sai dai kuma an gaza mantawa da tsohuwar al'adar tayar da hankali a gangami na yakin neman zaben.
Kuma kama daga jihohin Nasarawa zuwa ga Zamfara sannan da Kaduna daga baya dai an fara ganin kokari na gabatar da daba da tayar da hankali cikin yakin neman zaben. Duk da cewa, tayar da hankali yana zaman al'ada a siyasar tarrayar Najeriya a lokaci mai nisa, rabuwar addini da kabilar da ke fagen siyasa na kasar na dada jefa damuwa bisa duk wani rikicin da ke iya mamaye yakin neman zaben jam'iyyu a kasar.
Kuma tun ba a kai ga ko ina ba ake nunin yatsa a tsakanin jam'iyyun da ke dada zargin juna da haddasa tashin hankalin mai tasiri. Kokarin kunyata na gaba ko kuma fada na kai wa ya zuwa bakin hamma dai, koma ya take shirin da ta kaya a Zamfara, dabar da ta nemi tarwatsa wani gangami na jam'iyyar PDP a Kaduna, na kara fitowa fili da irin jan aikin da ke gaban 'yan mulki na kasar. Shi kansa shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya dauki lokaci yana kiran zama na lafiya cikin yakin neman zaben da ke da tasirin gaske a siyasa dama zamantakewa a kasar.
Koma ya take shirin da ta kaya a tsakani na masu neman zarcewar da kuma masu tunanin kwace goruba a hannun kuturu, dai kara tayar da hankali cikin fage na siyasar dai kuma a tunanin Faruk BB Faruk da ke sharhi bisa batun na siyasa, na nuna alamu na gazawar manyan jam'iyyun da ke nuna alamun ko mutuwa ko yin rai. Abun jira a gani na zaman iya kai wa ga toshe hanyar bullar tayar da hankali a Najeriyar da a baya ta sha da kyar cikin rikici na siyasar.