1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwan teku na ci gaba da mamaye doron kasa

November 28, 2023

Ruwan teku na ci gaba da canye kasar nomaa daida i lokacin da har yanzu kasashen duniya suka gaza aiwatar da yarjejeniyar yaki da dumamar yanayi ta Cop21 har ga ta COP 28 ta zo a Dubai amma kuma ba tabbas.

https://p.dw.com/p/4ZWhY
Hoto: Mick Tsikas/AAP/picture alliance

 A ranar (30-11-2023) ake bude taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 28 kan sauyin yanayi a Hadaddiyar Daular Larabawa, a Dubai. Wannan taro na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara fuskantar sauyin yanayi a duniya. Misali a Jamhuriyar Benin ruwan teku na ci gaba da mamaye kasa da ma wasu yankunan amma kuma har yanzu kasashen duniya sun gaza cimma matsayi  akan sauyin yanayi.

Teku na zaizaye kasa tare mamaye filayen noma wani abin fargaba ga duniya

Griechenland | Drohnenaufnahme Insel Milos | Sarakiniko Strand
Hoto: Frauke Scholz/imagebroker/Imago Images

 A gefen gabar tekun Benin,toroko na ruwan teku na cinye ƙasa ba tare da gajiyawa ba. Kasar ta kashe biliyoyin kudi na CFA a cikin 'yan shekarun nan don tabbatar da ganin cewar ta kiyyaye al'umma amma har yanzu abin ya gagara Raymond Mekpé, wani masunci ne: ''A da ruwan tekun ba nan suke ba suna can baya amma rashin kulawa ya sa da sannu a hankali tekun na ci gaba. Kowace rana, tana ci gaba da cinye kasa har ma da dukiyoyi da kadarori na gwamnati da na  sauran jama'a.

A ciki shekaru 21 Benin ta tafka mumunar asara da ba ta da misali

Israel entsendet Kriegsschiffe ins Rote Meer
Hoto: Israel Defense Forces/Anadolu/picture alliance

Tun daga shekara ta 2002, Benin ta yi hasarar daruruwan kilomita na kasa da teku ta mamaye, a cewar masanin ilimin teku Cossi Georges Dêgbé: ''Idan ba a yi wani abu ba, a cikin ƴan shekaru za mu rasa hanyar da ta hada tsakanin Cotonou da Porto-Novo ruwan teku zai mamayeta. Ba ma son hakan. A kwai bukatar dauki matakan kandgarki."

Benin ta kashe makudan kudade domin shawo kan lamarin amma har yanzu abin ya gagara

Nigeria Klimawandel und Wahl
Hoto: Katrin Gänsler/DW

 Kusan kudin CFA biliyan dari ne aka zuba  a cikin 'yan shekarun nan,domin yakar wannan bala'i sai dai Alain Tossounon, shugaban cibiyar sadarwa  ta fafufukar kare,muhalli da kuma yanayi ya ce waɗannan ƙoƙarin bai isa ba: "Dole ne a yau mu shigar da wannan al'amari cikin dukkan ayyukan da mu ke gudanarwa. Kuma mun yi imani,a  matsayinmu na kwararru, cewa a yau kokarin da ake yi bai wadatar ba kuma har yanzu al'umma ba su fahimci illar lamarin ba." Masana na cewar akwai fargaba a duniya a kan garuruwan da ke bakin teku wanda wata rana za a wayi gari ruwan tekun ya cinyesu duk wannan a kan sauyin yanayi, wanda har yanzu ksashen duniya ke yin tababa wajen cika alkarin da aka dauka tun a taron COP21 na yarjejeniyar Paris da aka cimma a shelara ta  2015.

Benin Erosion - MP3-Stereo