1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar taƙaddama cikin jam'iyyar MNSD Nasara a Nijar

Mahaman KantaNovember 6, 2014

Jam'iyyar ta sanar da dakatar da wasu manyan ƙusoshinta guda 35 saboda sun shiga cikin gwamnatin haɗin kan ƙasa.

https://p.dw.com/p/1DiPC
Seini Oumarou Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Afrika
Seini Oumarou shugaban MNSD NasaraHoto: MNSD

Wani sabon rikici ya ɓarke a cikin jam'iyar MNSD Nasara madigar adawar a Jamhuriyar Nijar, inda ta dakatar da wasu ƙusoshinta 35 har tsawon shekara daya.

Rikicin jam'iyyar ya samo asili ne bayan da wasu ya'yanta suka shiga gwamnati

Daga cikin waɗanda aka dakatar a kwai ministan ƙasa a fadar shugaban ƙasa Abuba Albade, wanda shi ne babban sakatare janar na jam'iyyar, da Alma Oumarou ministan kasuwanci, mataimakin shugaban jam'iyyar a jihar Damagaram.

Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Seini Oumarou shugaban MNSD NasaraHoto: DW/M. Kanta

Wannan mataki na zuwa ne ganin yadda waɗannan mutane ke ci gaba da zama cikin gwamnati alhali Jam'iyyar tasu na cikin adawa kuma ba tare da sun yi murabus ba.Tun farko jam'iyyar ta ce ta kori waɗannan 'yan siyasa amma daga bisani suka shigar da ƙara kotu ta soke korar. Jam'iyyar ta fara samun rarabuwar kawuna ne tun bayan da wasu ya'yanta suka shiga cikin gwamnatin haɗin kan ƙasa.

Mahamman Murtala,mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar ta MNSD ya ce sun dakatar da mutanen tsawon shekatra guda. To sai dai daga cikin waɗanda jam'iyyar ta dakatar Alma Umaru ya ce suna da ja a kan hukunci