Sakamakon taron Rasha da Iran a Moscow
February 21, 2006Rasha
Masu shiga tsakani na kasashen Iran da Rasha sun kammala tattaunawarsu na yini biyu a birnin Moscow,wadda keda nufin rage matsin lamba da tehran ke fuskanta daga kasashen duniya a dangane da harkokinta na Nuclear.Wakilan Iran dai sunbayyana tattaunawar da kasancewa mai faida,kuma an amince da sake cigaba da tattaunawara wani lokaci nan gaba.
To sai dai ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fadawa manema labarai cewa,da sauran lokaci na bayyana sakamakon wannan tattaunawan a dangane da amincewa sarrafa sinadran uranium wa Iran a Rasha.
Tun da farko dai ministan harkokin waje na Jamus Frank-Walter Steinmaier yayi fatan cewa hanyar diplomasiyya ce kada zata iya warware wannan rikici da Iran ta tsinci kanta ciki,saidai yayi gargadin cewa har yanzu akwai barazanar kakabawa Iran takunkumin tattalin arziki,sabanin hakan.To amma ministan harkokin wajen Iran yace,kasarsa bazata sake shiga wata tattaunawa da Britania da Faransa da Jamus na hadin gwiwa ba,amaimakon haka zata tattauna dai dai da kasashen na turai.