Saudiyya za ta yaki ta'addanci a duniya
November 27, 2017Talla
Yerima Muhammad bin Salman na kasar Saudiyya, ya lashi takobin kakkabe 'yan ta'adda sai ya ga iyakarsu a duk inda suke a duniya. Yerima bin Salman ya fadi hakan ne yayin da wakilan manyan kasashen Musulmai 40 ke halartar wani taro irinsa na farko kan hadin kai don yakar ta'addanci a masarautar.
Taron da ya hada ministocin tsaron kasashen na Musulmi da wasu manyan jami'ai, na zuwa ne yayin da ita babbar kawar Amirka wato Saudiyyar ke jagorantar fatattakar mayakan IS a kasashen Iraki da Siriya. Kasashen da suka hadun dai galibinsu, kasashe ne 'yan Sunni, kuma manyan kasashen Musulmi masu akidar Shi'a irinsu Iran da Iraki da Siriya dai ba su da wakilci a wannan taro.