An sake harbe wani matshi a Senegal
February 11, 2024Talla
Mutuwar matashin a jiya Asabar bayan harbin da 'yan sanda suka yi mishi a ciki ta janyo karin suka musamman ma daga bangaren 'yan adawa.
Wannan na zuwa ne bayan da shugaban kasar Macky Sall ya bayyana gaban jama'a karon farko tun bayan sanar da dage zabe ya yi watsi da zargin da 'yan adawa ke masa na cewar yana son ya makale a kan mulki ne ko ta halin kaka, Shugaba Sall ya bayyan takaicinsa da ya ce 'yan adawa na amfani da wannan damar dage zabe wajen tunzura al'ummar kasar.
Yanzu haka dai kungiyoyin fararen hula da na adawa sun shirya zanga-zanga a ranar Talatar da ke tafe a ci gaba da bijirewa matakin majalisa na dage zaben shugaban kasa.