Kotun tsarin mulki ta sanya ranar zabe a Senegal
March 7, 2024Kotun tsarin mulkin ta Senegal dai ta ayyana ranar 31 ga wannan wata na Maris da muke ciki, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasar, maimakon 24 ga watan Maris din da Shugaba Macky Sall ya sanar tare da jan hankali kan gudanar da zaben karkashin sharuddan da ta gindaya. Wannan lamarin na zuwa a daidai lokacin da majalisar dokokin kasar ta amince da kudrin dokar da ke yi wa wasu jiga-jigan 'yan adawar kasar afuwa.
Karin Bayani: Tattaunawar neman samun masalha a Senegal
Alkalan kotun dai, sun yi watsi ne da sakamakon taron warware dambarwar siyasar kasar da aka yi a ranakun 26 da 27 ga watan Fabarairun da ya gabata. Djibril Gningue, jigo ne a wasu kungiyoyin fararen hula masu kokarin ganin an gudanar da zaben gaskiya a Senegal, ya ce yana alfahari da irin karfin fada ajin da kotun tsarin mulkin kasar ke da shi. Shugaba Macky Sall ya rusa gwamnatin kasar a cikin wata sanarwar da majalisar ministocin ta fitar, tare da bayyana ranar 24 ga watan Maris a matsayin ranar da za a gudanar da zabe.
Sai dai masaniya kan harkokin mulki da huldar kasa da kasa Mame Diarra Ndiaye Sobel kana memba a kawancen Front de résistance FIPPU, ta bayyana cewa duk da jinkirin da aka samu ana iya shirya zaben shugaban kasar a kan kari. A hannu guda kuma bayan an dau dogon lokaci ana tattaunawa daga karshe majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin yin afuwa da shugaba Macky Sall ya gabatar mata, inda 'yan majalisun dokoki 94 suka amince yayin da 49 suka yi adawa kana uku suka yi rowar kurirsu.
Karin Bayani: 'Yan adawa za su kaurace daga taron Senegal
Amincewa da matakin mai cike da cece-kuce ka iya bayar da damar sakin 'yan adawa ciki har da Ousmane Sonko da Bassirou Diomaye Faye daga kaso, a cewar Alimou Barro mamba a jam'iyyar Pastef da ke goyon bayan takarar Bassirou Diomaye Faye a zaben shugaban kasa. Ana dai ganin akwai bukatar gaggauta soma aiki kan tsare-tsaren gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Senegal da ke da 'yan takara 19 da kotun tsarin mulki ta sahalewa tsayawa takara, domin maye gurbin Macky Sall.