Senegal za ta rufe sansanonin sojin kasashen ketare
December 27, 2024Talla
Firanministan Senegal, Ousmane Sonko ya ce shugaban kasar ne ya yanke hukuncin rufe dukannin sansanonin sojin kasashe ketare da ke kasar. A watan Nuwamban wannan shekarar ce shugaba Senegal, Bassirou Diomaye Faye na Senegal ya bayyana shirinsa na rufe sansanonin sojin Faransa a kasar.
Karin bayani: Shugaban Faransa Emmanuel Macron na son kulla alaka da sabon shugaban Senegal
Abun da ya sanya ake ganin matakin a matsayin abun da ya shafi Faransar kai tsaye. Senegal ta bi sahun kasashen Mali da Burkina Faso da Niger wajen juyawa uwargijiyasu Faransa baya. Sabuwar gwamnatin Senegal dai ta dauki matsaai mai tsauri kan kasancewar sojojin Faransa a kasar, abun da ake gani tamkar gadon danniya ne daga turawan mulkin mallaka.