Cikin shirin za a ji ana ci gaba da rikici tsakanin Falasdinawa da sojin Isra'ila a yankin gabar yamma ta kogin Jordan, bayan matakin ayyana birnin Kudus a matsayin fadar mulkin Isra'ila da shugaba Trump na Amirka ya yi. Sojin Isra'ilar dai na zargin kungiyar Hamas da kai masu farmaki, inda har suka ce sun yi harbe-harbe a wasu sansanoninsu biyu.