1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyarar aiki a Vietnam

Abdoulaye Mamane Amadou
August 28, 2023

Fadar White House ta sanar da ziyarar shugaban Amurka Joe Biden a Vietnam a wani yunkuri na kara inganta huldar diflomasiyyar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4Vg0I
Amurka I Joe Biden I Ziyara I Air Force One
Shugaban Amurka Joe Biden na sauka daga jirgin Air Force OneHoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

Kakakin fadar White House Karine Jean-Pierre, ta ce a ziyarar, Shugaba Biden zai yi tozali da takwaransa Nguyen Phu Trong da ke jagorancin kasar tare da duba hanyoyin inganta fasahohin zamani da na jami'o'i da ayyukan hannu, ba'idinsa da batun sauyin yanayi da na inganta zaman lafiyar yankin.

Ko a farkon Aguustan wannan shekarar ma sai da shugaban na Amurka ya bayyana a gaban kusoshin jam'iyyar Democrats da cewa  kasashen Philippines da Vietnam da Cambodia na kokarin kula hulda da Amurka a wani mataki na daga wa kasar China dan yatsa.