1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Kim ya gana da Putin

September 13, 2023

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya gana da takwaransa na Rasha Vladmir Putin yayin da shugabannin biyu suka isa tashar sararin samaniya ta Vostochny.

https://p.dw.com/p/4WGj0
Shugaba Vladmir Putin na Rasha da takwaran sa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un
Hoto: Vladimir Smirnov, Sputnik, Kremlin Pool Photo/AP/picture alliance

Kafofin yada labaran Rasha sun ruwaito cewa, Shugaba Putinya ce ya yi farin cikin ganin Shugaba Kim yayin da kuma aka ga shugabannin biyu sun yi musabaha. Shugaba Vladmir Putin ya kuma ce, zai taimaka wa Koriya ta Arewa ta gina tauraron dan Adam.

Karin bayani:  Kim Jong Un ya isa kasar Rasha

Ana sa ran shugabanin biyu su yi zaman tattaunawa bayan kammala rangadin tashar ta Vostochny kana su tattauna batun inganta dangantar tsaro da kuma samar da makamai.

Karin bayani: Kim Jong Un zai isa Moscow

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da a wannan Larabar Koriya ta Arewar ta harba makamai masu linzami biyu masu cin gajeren zango. Hukumomin Koriya ta Kudu sun ce an harba makaman ne zuwa tekun Japan.