Trump ya sallami Tillerson
March 13, 2018Shugaban Amirka Donald Trump ya sallami sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson daga mukaminsa. A wani sakon ba-zata da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban na Amirka ya ce ya maye Mr Tillerson din ne da shugaban hukumar tattara bayanan sirrin kasar CIA, Mike Pompeo. Tuni ma dai aka bayyana Gina Haspel a matsayin wacce za ta maye Mr Pompeo a hukmar ta CIA, mace ta farko da za ta jagoranci hukumar.
Wani jami'i a fadar White House ta Amirkar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce shugaba Trump ya dauki matakin ne a shirinsa na hada sabuwar tawaga a shirye-shiryen tattaunawar da Amirkar za ta yi da Koriya ta Arewa. An dai dade da rade-raden cewa akwai sabanin ra'ayi tsakanin shugaba Trump da Mr Rex Tiellerson din musamman kan harkokin da suka shafi kasashen Koriya ta Arewa da kuma Iran.