1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaban Afghanistan ya yi jawabi a kan rikicin Taliban

August 14, 2021

A karon farko Shugaba Ashraf Ghani na kasar Afghanistan ya yi wa 'yan kasar jawabi, tun bayan fara karbe yankuna da mayakan Taliban suka yi tsawon makonni.

https://p.dw.com/p/3yzKX
Afghanistan | Präsident Ashraf Ghani
Hoto: Sajjad Hussain/AFP/Getty Images

Shugaba Ashraf Ghani ya ce abin da aka sanya a gaba a yanzu, shi ne sake hada karfin dakarunta waje guda a daidai lokacin da ya rage kilomita 11 kacal mayakan Taliban su kutsa cikin Kabul babban birnin kasar.

Shugaban na Afghanistan ya ce an yi nisa a tattaunawa da ake yi wa wasu kasashen duniya a kokarin kawo karshen yakin da kasar ke ciki.

Kashi biyu cikin uku na kasar dai na hannun mayakan Taliban ne a yanzu, inda kasashe irin su Amirka da ma Faransa a baya-bayan nan ke gaggawar kwashe jami'ansu da ke a can.