1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Kokarin kawo karshen yakin basasa

Ahmed SalisuSeptember 10, 2016

Amirka da Rasha sun amince da wani tsari na kawar da tashin hankalin da ake fama da shi da a kasar Siriya wanda ya ki ci ya kuma ki cinye.

https://p.dw.com/p/1JzhL
US-Außenminister John Kerry und der russische Außenminister Sergej Lawrow
Hoto: picture alliance/ZUMA Press/State Department

Kasashen biyu suka ce tsagaiata da kuma neman mafita a siyasance ne wannan shiri zai fi maida hankali a kai. Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov suka ce idan wannan shiri ya tabbata to hakan zai kawo karshen kiki-kika din da ake fama da shi wajen warware rikicin kasar wanda aka shafe sharu da dama ana yinsa.

Kerry ya ce bayan da suka yi wani zama na tsawon sa'o'i 12, Rasha da Amirka sun fidda wani jadawalli wanda a ganinsu idan aka yi aiki da shi to za a kai ga cimma matsayar da aka jima ana son gani kan wannan rikici. Guda daga cikin abubuwan da ake son ganin an cimma shi ne bangarorin da ke rikici da juna a Sirya din su bada dama ta kai kayan agaji ga wanda suke cikin yanayi na bukata kuma tuni Rasha ta ce ta zanta da gwamnatin Assad wadda ta bada amincewarta kan yin hakan.