1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Siriya: Yaki ya yi kamari

December 6, 2024

Kungiyoyin kare hakkin 'dan adam da sauran masana na ci gaba da nuna damuwa da kuma fargaba, kan yadda 'yan tawayen Syria na HTS ke muzgunawa jama'a tsawon shekaru a yankunan da suke da iko da su.

https://p.dw.com/p/4nqgT
Hoto: Juma Mohammad/IMAGESLIVE via ZUMA Press Wire/picture alliance

A 'yan kwanakin nan ne kungiyar 'yan tawayen Syria ta Hayat Tahrir al-Sham wato  HTS ta sake farfadowa, tare da kwace wasu garuruwa masu matukar muhimmanci, cikinsu har da birni na biyu mafi girma a kasar wato Aleppo, da Idlib, inda kuma suka durfafi Hama, bayan murkushe jami'an sojin shugaba Bashar Assad. Kungiyar HTS wadda Amurka da kuma kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya suka jima da ayyana wa a matsayin ta ta'addanci, tana ci gaba da kutsawa tare da kai hare-hare a kasar Syria, a kokarinta na ganin ta  kawar da gwamnatin Shugaba Assad daga kan karagar mulki. tare da alkawarin kare martabar kowa a kasar, kamar yadda Chrissie Steenkamp, kwararriya a sha'anin siyasa da zamantakewa daga jami'ar   Oxford Brookes da ke Burtaniya ta yi tsokaci a kai: '' Suna nuna wa al'umma cewa akidarsu ba irin ta kungiyoyin ta'addanci kamar su ISIS da dangoginsu, da ke gallazawa tsiraru kabilu da addinai, ba su da nufin takurawa kowa, ko kiristoci ko wasu da akidarsu ba ta zo daya ba''.

Syrien Aleppo 2024 | Offensive syrischer Rebellen im Westen von Aleppo
Hoto: Juma Mohammad/AP Photo/picture alliance

To sai dai ga  Hiba Zayadin, babbar jami'ar binciken cin zarafin bil'Adama a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma arewacin Afirka a kungiyar kare hakkin 'dan Adam ta human Rights Watch, ta ce al'ummar Syria na tsoron shigo-shigo ba zurfi daga HTS: '' Yayin da HTS ta kuduri aniyar kare fararen hula, tare da jan hankalin dakarunta su martaba tsarin a yayin fafatawar, to amma tsiraru kamar Kurdawa Kiristoci da Alawite masu tushe daga Shi'a, na tababar samun tabbacin hakan, idan aka yi la'akari da yadda HTS da takawararta ta SNA mai samun goyon bayan Turkiyya suka jima suna cin zarafin jama'a ba gaira ba dalili a Syria. Ciki har da lalata wurare na tarihin addinai da al'adu:''

Syrien Region Aleppo | Vormarsch von Dschihadisten gegen Regierungstruppen
Hoto: RAMI AL SAYED/AFP

A shekarar  2011 aka kirkiro kungiyar HTS, mai alaka da Al-Qaeda, kuma daga baya suka raba gari sakamakon sabanin manufa.Jerome Drevon na kungiyar ICG mai binciken kwakwaf, wanda har ma ya taba ganawa da jagororin HTS, ya ce kungiyar ta fara bude kofofinta ga sauran addinai don samun karbuwa daga gare su: ''Tsawon lokaci HTS na tuntubar jagororin wasu addinan, inda suka gana da wakilan Kiristoci don jin bukatunsu, wanda suka mayar wa matsugunansu da filayensu na yankin Idlib da aka kwace a baya. Sannan tun daga shekarar ta 2018 zuwa yanzu suna samun zarafin gudanar da bukukuwansu na Kirsimeti, haka batun yake ga mabiya Druze.'' Shekaru 14 kenan da barkewar yakin basasar Syria, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu dari biyar, tare da ragargaza kasar. Kididdiga ta nuna cewa kasar na da mutane miliyan 25, kashi 70 cikin 100 masu bin tsarin Sunni, 13 cikin 100 'yan Shi'a, sai kashi 10 cikin 100 'yan Alawite da ke da tushe daga Shi'a, da sauran tsirarun Kiristoci da Druze da kuma  Kurdawa.