1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Syria ta shiga mawuyacin hali na yaki da 'yan tawaye

December 1, 2024

Shugaba Bashar al-Assad na kasar Syria ya sake lasar lakobin kare dayantakar kasarsa, musamman ma a wannan lokaci da gwamnati ke fama da barazanar mayakan tawaye.

https://p.dw.com/p/4ncAJ
'Yan tawayen Syria sun kwace birnin Aleppo
'Yan tawayen Syria sun kwace birnin AleppoHoto: Anas Alkharboutli/dpa/picture alliance

A ranar Asabar ne dai rahotanni suka tabbatar da cewa mayakan da ke jayayya da gwamnatin ta Syria sun kwace iko da kusan ilahirin birnin Aleppo, wanda ke na biyu mafi girma a kasar.

Gamayyar kungiyoyin tawaye karkashin inuwar kungiyar Hayat Tahrir al-Sham, su ne suka gama karfi wajen fatattakar mahukunta ciki har da kwamandojin yakin gwamnati daga birnin.

Sama da mutum 300 ne da suka hada da fararen hula suka mutu, tun bayan barkewar sabon artabu a ranar Laraba, kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin 'yan Syria wato Syrian Observatory for Human Rights ta tabbatar.

Kasar Rasha da ke taimaka wa Syria a yakin da take yi, ta ce ta aika da wasu jirage domin taimakawa wajen yaki da mayakan na tawaye a kasar.