1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Chadi sun kashe 'yan Boko Haram da dama

November 8, 2024

Wasu hare-hare ta sama da sojojin Chadi suka kaddamar, sun salawantar da mayakan Boko Haram tare da jikkata da dama, a cewar shugaban kasar Mahamat Idriss Deby Itno.

https://p.dw.com/p/4mntU
Dakarun gwamnatin kasar Chadi
Dakarun gwamnatin kasar ChadiHoto: Str/AFP

A wata ganawar da ya yi da manema labarai, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ya ce shi ma da kansa ya jagoranci hare-haren ramuwar gayya da aka kai maboyar Boko Haram da ke a kusa da iyakar kasar da Najeriya, sai dai kuma bai bayyana adadin 'yan tarzomar da aka kashe ba.

Kafin yanzun dai kasar ta Chadi ta lashi takobin durkusar da Boko Haram, musamman a yayin kaddamar da wani sabon sintirin soji da aka yi cikin watan Oktoba, a lokacin da Boko Haram suka kashe gomman sojojin Chadi a barikinsu.

A shekara ta 2015 ne dai Chadin da makwabtanta Najeriya da Nijar da Kamaru, suka girka runduna ta hadin gwiwa mai dakaru 8,500 domin yaki da Boko Haram, sai da a baya-bayan nan dakarun na Chadi na cewa za su janye saboda dalilai na rashin samun cikakken hadin kai a tsakaninsu.