Salon rayuwaNajeriya
Kaduna: Taimakon makarantun almajirai
November 14, 2024Talla
Kiristocin wannan Mujami'a karkashin jagorancin Pastor Yohanna YD Buru dai, na fatan ganin yara almajirai sun zurfafa ilminsu na addini da da na zamani kamar sauran yaran da ke zuwa neman ilmi a fadin duniya. Pastor Buru ya jagoranci tawagar mabiyansa zuwa wata tsangaya, ya bayyana cewa sun sayo Alluna da Tawada da Alkalami domin rarrabawa wadannan yara almajirai, domin suma suna da hakkin da ya wajaba akansu wajen tallafa wa ilmin wadannan yara.