1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

'Yan Najeriya na kara tsunduma cikin talauci

Muhammad Bello
June 16, 2021

Wani sabon Rahoto da Bankin Duniya ya fitar, ya ce tsadar rayuwa da hauhawar farashi na ci gaba da mummunan tasiri a tattalin arzikin Najeriya kuma haka ya tura kara tura 'yan Najeriya miliyan bakwai cikin halin talauci.

https://p.dw.com/p/3v3HR
Nigeria Lagos Stadtansicht
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Bankin dai ya ce in har hukumomi ba su kai ga yin hattara ba ,musamman ta fannin aiwatar da sauye sauyen manufofi ma su inganci a harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudade, tattalin arzikin kasar ka iya samun ci gaba amma cikin yanayi na tafiyar hawainiya. Bankin dai ya nunar, rashin ayyukan yi da yai katutu, yanayi ne da ke dada jefa da daman musamman matasa cikin halin aikata muggan laifuka irin su sace-sace da garkuwa da mutane dan neman kudaden fansa a kasar.

Karin Bayani:Najeriya na ci gaba da shiga matsaloli

Nigeria - Abuja tomato traders
Hoto: DW/S.Olukoya

To kan wannan rahoto da Bankin na Duniya ya fidda ne ,na jiwo bakunan wasu 'an Najeriya masana da da wadanda dai 'yan Najeriya ne. Kuma galibi suna da ra'ayoyi mabanbanta kan matsalolin da ake ciki gami da hanyar da suke gani a samu mafita.

Kuma wasu na ganin dama daya daga dalilan da ke haifar da rashin tsaro shi ne talauci. Yayin da tura ta kai bango, to komai na iya faruwa. Kaso kimanin 80 cikin 100 na wadanda ke aikata laifuka, ka iya barin mummunar halayyar, matsawar an kula da su. Dan haka wannan rahoto na Bankin Duniya ,kamata yai gwamnati ta dube shi sosai don nazari,da zai kai ga kokarin kawar da aikata muggan laifuka ta hanyar habaka tattalin arzikin kasa, da tallafawa matasa marasa aiki da kuma ba da shugabanci na gari.