Taliban ta kulla huldar kasuwanci da Rasha
September 28, 2022'Yan Taliban da ke tsattsauran ra'ayin Islama a Afganistan suka ce sun kulla yarjejeniyar kasuwanci ta farko da kasar Rasha. A lokacin da yake karin haske a birnin Kabul, ministan ciniki da masana'antu na Afghanistan Haji Nuruddin Asisi ya bayyana cewar gwamnati a birnin Moscow ta yi musu rangwame farashin kayan masarufi idan aka kwatanta da na kasuwannin duniya.
Wannan yan nufin cewar Rasha za ta shigar da kusan tan miliyan daya na man fetur, tan miliyan daya na dizal, ton 500,000 na iskar gas da tan miliyan biyu na alkama a duk shekara a kasar Afghanistan. Babu wani sharhi ko martani da aka samu daga bangaren Rasha a kan wannan batu.
Amma dai wannan nai zama babbar yarjejeniyar tattalin arziki ta farko da 'yan Taliban da ke mulki a Afghanistan suka kulla tun bayan da suka koma kan karagar mulki fiye da shekara guda da ta wuce.