1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta nace sai Ukraine ta yi aiki da manyan makamai a Rasha

September 19, 2024

Kasashen Turai masu wakilci a kungiyar EU masu yawa sun bukaci da a sakar wa Ukraine mara wajen ganin ta kare kanta da manyan makamai daga hare-haren kasar Rasha a kanta.

https://p.dw.com/p/4kqle
Shugabar hukumar Turai, Ursula von der Leyen
Shugabar hukumar Turai, Ursula von der LeyenHoto: FREDERICK FLORIN/AFP

'Yan majalisar dokokin Tarayyar Turai, sun yi kiran da a janye haramcin da aka dora wa Ukraine na amfani da makaman yaki da kasashen yammacin duniya suka samar mata, makaman da aka tsara kasar za ta yi amfani da su a kan wasu yankuna na Rasha.

Matakin dai ya dakatar da Ukraine din ne daga samun sukunin kare kanta yadda ya dace daga hare-haren Rasha da ke shafar al'uma da kuma muhimman gine-ginen kasar, a cewar majalisar dokokin ta Turai.

Kuduri ne dai da ya samu goyon baya daga 'yan majalisar EU su 425, a taron da suka yi a Strasbourg na kasar Faransa, inda 131 suka kasance wadanda suka bijire wa bukatar, wasu mutum 63 kuwa ba halarci zaman ba.

Zaman majalisar ya kuma bukaci da a tsawaita wa'adin dora wa Rasha da kawayenta takunkumai na karya tattalin arziki kan mamayar da ta yi wa Ukraine.