1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai za ta kara wa manoma kudade

September 13, 2024

Kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai EU za su kara yawan kudaden da suke warewa domin bai wa manomansu, kamar yadda hukumar Turai ta sanar a yau Juma'a.

https://p.dw.com/p/4kbYp
Lokacin zanga-zangar manoma a Jamus
Lokacin zanga-zangar manoma a JamusHoto: Reuters/T. Schmuelgen

Wannan shirin bai wa manoman kudade ya biyo wata zanga-zanga ne da kungiyoyin manoman suka yi a wasu kasashen EU a farkon wannan shekara, inda suka nemi da a yi gyara ga tsare-tsaren da suka shafe su da ma wasu matakai kan sauyin yanayi da ake dauka.

Hukumar Turai ta ce manoma na iya samun karin kaso 70% na kudade kai tsaye, da kuma zai fara aiki daga watan gobe na Oktoba.

Haka ma ga wadanda harkoki na kiwon dabbobi, Tarayyar Turai ta ce za ta samar musu da kudaden da suke iya kaiwa kashi 85%.

Kafin yanzun dai manoma da makiyayan da ke kasashen mambobin Tarayyar Turan, na samun kaso 50 da kuma 70% na kudaden daga mahukunta.