1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin tsakanin shugaban Rasha da shugabannin Afirka

Mohammad Nasiru Awal
October 25, 2019

Jaridun sun mayar da hankali a kan taron kolin da aka yi tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin da shugabannin Afirka a Sochi da ke kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/3RwCY
Russland | Erster Afrika-Russland-Gipfel
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/Sputnik/Pool/Tass/A. Druzhinin

A labarin da ta buga jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce a ranakun Laraba da Alhamis Shugaba Putin ya karbi bakoncin shugabannin kasashe 43 na Afirka da wakilai na wasu shugabannin da ba su halarci taron da ke zama na farko da Rasha ta shirya. Jaridar manufar taron ita ce Rasha na neman angizo a nahiyar Afirka sai dai masana sun yi suka cewa Rasha ba ta da wata manufa ta a zo a gani ga Afirka. A halin yanzu dai Rasha na taimaka wa wasu kasashen Afirka gina tashoshin makamashin nukiliya sai kuma makamai da sojoji da take turawa a wasu kasashen kamar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda sojojinta ke horas da sojojin kasar mai fama da tashe-tashen hankula.

Russland | Erster Afrika-Russland-Gipfel |  Mi-35P
Hoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/E. Lyzlova

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhi kan sabuwar dangantakar da Shugaba Putin ke son kulawa da kasashen Afirka. Jaridar ta ce taron na birnin Sochi ya mayar da hankali kan albarkatun karkashin kasa kamar man fetur, da lu'ulu'u da alkama da makamai da ma kokarin samun angizon siyasa a Afirka. Sai dai ta ce yanzu haka harkar kasuwanci da kasar ke yi da Afirka ba ta fi ta Dala miliyan dubu 20 ba, idan aka kwatanta da kimanin harkokin kaauwanci na kimanin Dala miliyan dubu 200 da kasar China ke yi da nahiyar ta Afirka.

Hakazalika Rashar ba ta da hajoji da yawa da Afirka ke bukata. Jaridar ta kara da cewa Rasha ba za ta iya samun irin tasiri da tsohuwar Tarayyar Sobiet ta yi a Afirka ba, inda bayan makamai da taimako na siyasa ta kuma ba wa Afirka taimakon raya kasa. Kuma ma wannan taron ya makaro domin tun shekarar 2006 kasar China ke gudanar da irin wannan taro da kasashen Afirka. Yayin da a shekarun baya dalioban Afirka suka yi karatu a jami'o'in Tarayyar Sobiet, yanzu 'yan Afirka sun gwammace su tafi China.

Burundische Flüchtlinge fliehen vor Gewalt und den politischen Spannungen Burundis nach Tansania
Hoto: AP/J. Delay

Tanzaniya na mayar da 'yan kasar Burundi gida inji jaridar Neue Zürcher Zeitung sannan sai ta ci gaba da cewa kimanin 'yan gudun hijira dubu 200 ne za su koma Burundi da ke cikin hali na rashin tabbas. Jaridar ta ce kaura daga Burundi zuwa Tanzaniya ta fara tun a farkon shekarun 1960 bayan samun ‘yancin kai. Sannan kuma a lokacin kisan kare dangi da rikicin siyasa dubun dubatan 'yan Burundi sun yi hijira zuwa Tanzaniya. Watannin biyu da suka wuce gwamnatocin kasashen biyu sun ce dole 'yan gudun hijirar Burundin su koma kafin karshen wannan shekara. Sai dai duk da cewa a zahiri babu wani matsi na komawa da su gida yanzu amma a wani abin da ke kama da kora da hali, a dole 'yan Burundi na tashi daga sansanonin 'yan gudun hijira musamman na kusa da kan iyaka da Tanzaniya suna komawa gida. Domin ana rufe kasuwanni da shaguna kuma abinci ya yi karanci a sansanonin. Sannan hukumomin Tanzaniya na kara takaita aikin kungiyoyin agaji a yankunan na ‘yan gudun hijirar Burundi.

Kariba-Staudamm auf der Grenze zwischen Sambia und Simbabwe
Hoto: picture-alliance/WILDLIFE/Harpe

A karshe sai kasar Zimbabuwe inda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta tabo matsalar yunwa da ke barazana ga miliyoyin 'yan Zimbabuwe a daidai lokacin kasar ke fuskantar matsalar kamfar ruwa. Jaridar ta ruwaito kungiyoyi agaji na cewa kimanin mutum miliyan 5.5 a kasar ba za su abin sakawa bakin salati ba ya zuwa karshen shekara, yanzu haka ma wasu miliyan 3.5 ne karancin abincin ya shafa. Gwamnatin kasar ma ta tabbatar da wannan labari ta ce ana bukatar fiye da  tan dubu 900 na hatsi a kasar.