Tashin hankali bayan bidiyon daliban da aka sace
April 28, 2021Kwanaki biyu ke nan da fitowar wannan sabon faifan bidiyo wanda masu garkuwa da daliban makarantar horar da aikin gona ta gwamnatin Najeriya da ke a garin Afaka- mando kaduna suka fitar. Wannan alamari dai ya sake jefa iyayen yara da sauran dangi fadawa cikin wani yanayi, da fargaba sakamakon yadda suka ga ‘ya’yansu a cikin dajin Kaduna a hannu masu garkuwa da su dauke da manyan makamai duk sun firgita.
Mallam Abdullahi Tumburka ke zama sabon shugaban kungiyar iyayen yaran da aka sace a Kaduna, ya bayyana kaduwa bisa ga yadda ya ga yaran a cikin wani munmunar yanayi da rashin kyan gani da kuma rashin koshin lafiya.
Mr Joshua Kurmi Pyan jikokinsa ne guda biyu, masu garkuwa suka sace a makarantar da ke nuna takaicin sa biga yadda iyayen yaran suka ga sabon bidiyon da aka aiko masu. Ya kara da cewa kamar yadda suka ga ‘ya’yan suna rokon yi duk abin da za a iya dan ceto su. Akwai wasu daliban na jami'a mai zaman kanta da ke hannu masu garkuwa da mutanen.
Karin Bayani:Najeriya: Yawaitar garkuwa da mutane
Masana tattalin arzikin kasa da jakadun zaman lafiya tare da kwarraru a bangaren sun nunar da cewa muddun dai hukumomi ba su tashi tsaye dan kawo karshen matsalar tabarbarewar tsaro ba, to babu shakka yankin arewa zai fada cikin wani yanayi, lamarin da suke ganin cewa lokaci ya yi na tattaunawa da duk ‘yan bindiga da sauran masu dauke da makamai dan ceto kasar daga fadawa ga matsaloli daban-daban.