Tinubu ya kaddamar da majalisar zartarwa
August 21, 2023Daya bayan daya sabbabin yan majalisar ministoci ta kasa suka rika yin rantsuwar kama aiki a wani bikin da ya samu halarta ta kusan daukacin masu ruwa da tsaki da mulkin kasar. Kama daga batun tattalin arziki zuwa tsaro, daukacin yan kasar na jiran cikon alkawarin sabuwar gwamnatin da ke da taken farfado da fata ga kasar. Fatan kuma da sannu a hankali yake kara dusashewa sakamakon kamun ludayin gwamnatin. Kama daga zare tallafin man fetur ya zuwa rikicin diplomasiyyar Nijar akwai alamun raba gari a tsakanin Abujar da mafi yawan talakawan da suka taka rawa wajen bullar sabuwar gwamnatin.
Karin bayani: Korafe-korafe dangane da nadin ministocin Tibunu
To sai dai kuma a cikin tsami na furar akwai babbar dama a bangaren talakawan a fadar Atiku Bagudu dake zaman sabo na minista na tattali na arzikin kasar. Kwazo cikin batun talauci ko kuma kara nisa cikin ruwan maras dadi dai, da dama a cikin sabbin ministocin sun hau aikin ba tare da kwarewar da yan kasar ke fata su gani ba.
Badaru Abubakar dai na zaman sabon ministan tsaron kasar da bashi da ilimin aikin soja ko kuma duk wata harka ta tsaro. To sai dai kuma ya ce shekaru takwas na mulkin Jigawa ya shirya shi kan sabon aikin da ke zaman mai girma. Koma ta ina sabbin ministocin ke shirin su bi wajen komawa saiti dai, sabbin masu mulkin kasar suna da babban aiki na kwantar da hankula da kila ma burge talakawan da suke zaman jira na shekaru kusan hudu.
Karin bayani: Tinubu ya kafa dambar yaki da cin hanci
A baya dai ana dada nisa kuma ana dada samun rabuwa a tsakanin mahukuntan da ma talakawan da ke tunanin yaudara cikin harkar mulkin. Mohammed idris dai sabon ministan labarai kuma kakakin gwamnatin da ke fadin sun san hanyar tunkarar kowa.
Abin jira a gani dai na zaman yadda ta ke shriin kayawa a tsakanin masu mulkin kasar da masu fatan sauyin na iya sake mai da fatan inganta rayuwa cikin kasar.