1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya fara daukar matakai kan Koriya ta Arewa

April 24, 2017

Shugaban na Amirka ya yi kiran kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya yi shirin kakaba takunkumi kan Pyongyang saboda abin da ya ce na barazanar gwajin man'yan makaman nukiliya da masu linzami.

https://p.dw.com/p/2bq8n
USA Trump - Giftgasangriff in Syrien
Hoto: picture-alliance/R. Sachs/CNP/AdMedia

Kiran na shugaba Trump dai na zuwa ne yayin da kusoshin gwamnatin Amirka ke shirin zama na musamman a jibi Laraba kan sa in sar da ke tsakaknin kasar da Koriya ta Arewa. Taron da zai hada da ministoci da hafsoshin soja da daraktocin leken asiri da kuma sanatoci 100 na kasar, ganawar da ba a saba yin irinta ba. Jami'an Amirkan dai na ci gaba da nuna damuwa kan matsayin Koriya ta Arewa dangane da makaman da ta ce babu makawa sai ta yi. A cewar Mr. Trump yunkurin na Koriya ta Arewa babbar barazana ce ga duniya da kuma ke bukatar hannu da yawa.