Trump zai sake ganawa da Putin
July 20, 2018Talla
Fadar Kremlin ba ta riga ta mayar da martani ba, sai dai zai kasance karon farko da wani shugaba na Rasha zai kai ziyara a fadar ta White House a kusan shekaru goma. Dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta yi tsami, bisa adawa da Amirka ke yi da rawar da Rasha ke takawa a rikicin kasar Ukraine da Siriya da kuma zargin da a ke ma ta na yin kutse a zaben shugaban kasar Amirka na shekarar 2016.