Tsamin danganta tsakanin 'yan jarida da 'yan siyasa
May 28, 2019
Kafafen yada labari sun kasance babban ginshiki wajen tafiyar da mulkin dimukaradiyya, amma kwarraru a taron birnin Bonn sun bayyanan cewa alakar da ke tsakanin masu yada labarai da 'yan siyasa ta yi hannun riga. Wata babbar matsala da ake fiskanta ita ce ta kasashen da ke ikirarin samun ci gaba a bangaren tsarin dimukaradiyya, inda 'yan jaridansu ba su da 'yancin fadin duk abin da suka ga jama'a na son ji.
Can Dündar shi ne tsahon babban editan jaridar Jamhuriyat (Cumhuriyet) na Turkiyya wanda yanzu haka yake gudun hijira a kasar Jamus bayan sakoshi daga fursunar kasarsa. Sai dai Dündar ya bayyanan cewa baya ga kasashe irionsu Turkiyya, 'yan jarida ko a kasashen Turai ba su da 'yancin walwawa. Inda ya bada misali da abin da ya faru kwanan nan a kasar Faransa.
Ya ce "Dubi Faransa inda kwannan nan mai gabatar da kara ya gayyaci dan jarida sabo da kawai ya rubuta labari bisa cinikin makamai tsakanin Faransa da Yemen. Don haka akwai matsalolin samar da 'yancin kafafen yada labarai ko da a Turai ne, don haka matsala ce da dukaninmu za mu hada kai don yakarta."
Georg Mascolo, Daraktan bincike na hadin gwiwar wasu manyan kafafen yada labaran kasar Jamus da suka hada da gidan talabijin na WDR; da NDR da kuma jaridar Süddeutscher Zeitung, ya ce Jamus na taka tsantsan bisa tarihinta na kasar. Ya ce
"Zan ci gaba da jan hankali cewa, dole kowane lokaci abu guda da gwamnati kamar Jamus ya kamata ta yi shi ne, ta ci gaba jajurcewa wajen kare dimukaradiyya da 'yancin fadan albarkacin baki, bisa sanin tarihin kasar".
Babbar mastalar da aikin jarida ke fuskanta shi ne, yadda 'yan siyasa ke rufe idonsu domin biyan bukatar kanfanoninsu a kasashen da ake mulkin kama karya. Don haka tun da batun tattalin arziki ya shigo ciki, neman 'yancin 'yan jarida ya kau. A cewar Galina Malishevskaya, fitacciyar 'yar jarida a kasar Belarus. Ta ce "Akwai babbar matsala kasancewar bangaren tattalin arziki da kuma na aikin jarida wuri guda. Abu ne mai matukar wuya idan aaka zo bangaren huldar kasar da kasa"
Michael Dobbs ya kasance dan majalisar dokokin Birtaniya da ya yi fici wajen sukar tsarin tafiyar da mulki da ke gudana yanzu haka a kasashen yamma, ya kuma bayyana cewa kamata ya yi 'yan jarida su tsaya kan aikinsu domin dama haka sana'ar ta gada. Ya ce " Zan iya tuna cewa a bisa tarhi 'yan jarida ba abokan 'yan siyasa ba ne. A tarihance kullum 'yan jarida da 'yan siyasa suna samun sabani da juna, kuma ya kamata su ci gaba da samun sabani domin alama ce ta zaman lafiyar al'umma."
Wani abin da aka fahimta a zahiri shi ne, akwai bambanci tsakanin fadin albarkacin baki da kuma sakar wa 'yan jarida mara.