1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon jagoran Soviet, Gorbachev ya rasu

August 31, 2022

Marigayi Gorbachev wanda ya taba karbar lambar yabo ta Nobel, da ake dauka a matsayin guda daga cikin dattawan karni na 20 ya rasu bayan doguwar jinya.

https://p.dw.com/p/4GFj5
Michail Gorbatschow
Hoto: Vasily Maximiov/AFP/Getty Images

An sanar da mutuwar tsohon jagoran tarayyar Soviet, Michail Gorbachev yana da shekaru 91.

Babban asibitin birnin Moscow, ya ce Gorbachev ya mutu ne da yammacin Talata, bayan fama da ya yi da doguwar jinya ta ajali.

Marigayi Gorbachev wanda ya taba karbar lambar yabon zaman lafiya ta Nobel, mutum ne da ake dauka a matsayin guda daga cikin dattawan karni na 20.

Tsare-tsaren marigayin ne suka samar da fahimta tsakanin tarayyar Soviet da kasashen yamma a zamanin yakin cacar baka.

Kokarinsa na daga cikin abin da ya kawo hadewar Jamus gabas da ta Yamma.

Marigayi Michail Gorbachev dai ya jagoranci tarayyar ta Soviet ne a tsakanin shekarar 1985 zuwa 1991.