1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe na juyayin rashin Robert Mugabe

September 6, 2019

A wannan Juma'a ne hukumomi a Zimbabuwe suka sanar da mutuwar Robert Mugabe tsohon shugaban kasar wanda ya jagoranci kasar zuwa tafarkin 'yanci daga 'yan mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/3PAr4
Robert Mugabe Simbabwe Afrika ehem. Präsident
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Marigayi Robert Mugabe, wanda ya yi wa siyasar Zimbabuwe mamayar kusan shekaru 40, ya bar mabambantan tarihi a zukatan ‘yan kasar inda wasu ke ganinsa a matsayin fitinannen shugaba wasu kuwa kallon suke masa na gwarzon da ya sama wa kasar ‘yanci daga turawan Birtaniya da suka yi wa kasar mulkin mallaka.Wasu daga cikin masu sukar tsare-tsarensa, na cewa mutum ne mai rauni ta fuskar gudanar da tattalin arziki da zarginsa da cin hanci da rashawa sai kuma wasu laifuka masu nasaba da take hakkin bil adama. Daga cikin zargin da ya yi karfi kan marigayin shugaban na Zimbabuwe, har da wani kamfe da ya kaddamar a shekarun 1980, da ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutum dubu 20 wadanda ke adawa da gwamnatinsa.

   Mugabe ya yi kaurin suna wajen yaki da manufofin kasashen ketare

Bildergalerie Robert Mugabe Simbabwe Afrika
Robert Mugabe a yayin wata ziyarar aiki a BirtaniyaHoto: picture-alliance/dpa

Marigayi Mugabe ya sha furta  cewa ''Ina dalilin ci gaba da kasancewar kamfanonin Birtaniya har 400 a Zimbabuwe, wadanda kuma Birtaniyar ce ke samun amfaninsu ba kasa ba. Ya za mu ci gaba da kasancewa da kamfanonin da kasashe irinsu Amirka da Birtaniya ke taimaka wa a kasarmu, suna aikin son ransu ba tare da suna biya ba, sannan mu kuma ba za mu rama ba?  Lokaci ya yi da mu ma za mu rama" Mulkin Robert Mugabe ya zo karshe ne cikin wani yanayi na rudani, bayan tsare shi a gida da sojoji suka yi a ranar 15 ga watan Nuwambar 2017, kafin daga bisani su sauke shi daga mukamin shugaban jam’iyyar ZANU-PF. Sojojin sun kuma yi barazanar tsige shi muddin ya ki yin murabus daga mukaminsa na shugabancin kasa.

  Robert Mugabe ya murabus sakamakon matsin lamba

Simbabwe Mugabe bei TV-Ansprache mit seinen Generälen
Shugaba Robert Mugabe na jawabi tare da wasu hafsosshin sojan kasarHoto: Getty Images/AFP/Str

A ranar 21 ga watan na Nuwambar ce a aka fito da sanarwar murabus din marigayi Robert Mugaben, koda yake daga bisani ya karyata batun, a daidai lokacin da dama daga ckin al’umar kasar sun nuna kosawarsu da mulkin shekaru 37 da ya yi a Zimbabuwe. Mugabe ya rasu ne yana da shekaru 95. Wasu shugabannin kasashen Afirka irinsu Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da kuma Uhuru Kenyatta na kasar Kenya sun bayyana shi a matsayin jarumin jagora kuma mayakin da ya tsaya wa kasarsa ta haihuwa wato Zimbabuwe.