Ko Afirka za ta yi maraba da Ukraine?
July 1, 2024Dangantaka tsakanin Rasha da kasashen Afirka dai, ta samo asali ne tun lokacin tshohuwar Tarayyar Soviet. Sai dai tun bayan darewa madafun iko sama da shekaru 10, Shugaba Vladmir Putin ya kara karfafa ta da ma kara lalubo sababbin hanyoyin ganin tasirin Rasha a nahiyar ya karu. Sai dai masu fashin baki kamar dan jarida dan asalin kasar Ukraine kuma masanin dangatakar kasa da kasa Illiya Kusa kamar sun makara, domin rashin huldarsu da kasashen Afirka na da matukar illa ga dangantakar diplomasiyya koda yake yanzu sun farga.
Karin Bayani: Karin iskar gas daga Najeriya zuwa Turai
Amma a cewar wani dan jaridar Najeriya Ovigwe Eguegu kafin mamayar Rasha a Ukraine, babu alaka mai karfi tsakanin Kiev da kasashen Afirka. Ya kara da cewa hasali ma ofisoshin jakadancin Ukraine 10 ne kadai a Afirka, yayin da Rasha ke da 43. Yanzu haka Ukraine ta bude sababbin ofisoshin jakadanci shida, kuma karin wasu na nan tafe. Ana dai ganin wannan nuna halin ko-in-kula da Ukraine ta yi a kasashen Afirka, ya janyo mata rashin samun amincewarsu a zauren Majalisar Dinkin Duniya yayin da ta bukaci su kada kuri'ar tilasta Rasha ta fice daga yankunan kasar da ta mamaye.
Nahiyar Afirka a zauren majalisar dai, ta fi kowace nahiya yawan masu zabe idan bukata ta taso. Duk a kokarin yin gogayya da Rasha da Ukraine ke yi a Afirka, tuni mahukuntan na Kiev suka fara isar da tallafin abinci ga wasu kasashe ciki har da Najeriya da Habasha da Kenya da kuma Somaliya. Ukraine dai na zaman kasa ta biyu a duniya da ta ke samar da masara ga Afirka, kuma kasa ta uku a duniya da ta ke samar da alkama a nahiyar. Hakan ya kara nuna irin rawar ganin da take iya takawa ta fannin samar da isasshen abinci a nahiyar.
Karin Bayani: Ukraine na kokarin karfafa hulda da Afirka
Amma kuma masanin harkokin diplomasiyar kasashen duniya Iliya Kusa ya ce, akwai bukatar kasarsa ta kara zage damtse da ma fadada a wasu fannonin. A bayyane yake Ukraine ba ita kadai ce ke rububin inganta dangantakarta da Afirka ba, a baya ministan harkokin kasashen ketare na Rasha ya ziyarci wasu kasashen nahiyar har sau biyu. Babban abun abin tamabaya a nan dai shi ne, ko Ukraine din za ta iya mamayar Rasha ta fuskacin tasiri a nahiyar Afirkan? LOkaci ne kawai zai nuna.