Ukraine ta ayyana ranar hadin kan kasa
February 15, 2022Talla
A safiyar Larabar za a yi sama da tutoci tare da rera taken kasar don nuna wa duniya hadin kai da 'yan kasar ke da shi. Hukumomin leken asirin Amirka dai sun yi gargadin cewa ta yiwu Rasha ta fara mamaya a ranar Larabar.
Kazalika ana sa ran Firanministan Japan Fumio Kishida zai gana da shugaba Zelensky ta wayar tarho, yayin da Tokyo fadar gwamnatin Japan din ta nuna damuwarta game da barazanar mamaya da Ukraine ke fuskanta daga Rasha. Dama dai Tokyo ta sha alwashin bin sahun sauran kasashen Turai wajen kakaba takunkumi ga Rasha, idan har ta cimma manufarta kan Ukraine.
Tuni ita ma Amirka ta sanar da mayar da offishin jakadancinta daga babban birnin Ukraine Kiev zuwa birnin Lviv da ke kusa da iyakar Poland.