1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSomaliya

Wani harim bom ya haddasa mutuwa a Somaliya

August 3, 2024

Wasu mahara da ake zargin na tarzoma ne sun kai hari a daren Juma'a a Somaliya inda bayanai ke tabbatar da mutuwar mutane da dama. Harin dai ya shafi wani Otel ne da kuma wani waje na shakatawa.

https://p.dw.com/p/4j4UO
Wajen da aka kai wa harin bom a Somalia
Wajen da aka kai wa harin bom a SomaliaHoto: Hassan Ali Elmi/AFP via Getty Images

Rahotannin da ke fitowa daga Somaliya, na cewa wasu mahara sun kai hari a wani Otel da ke Mogadishu babban birnin kasar inda akalla mutane 14 suka rasa rayukansu.

'Yansanda sun ce harin da ya shafi wani wajen shakatawa na Lido Beach, ya kuma jikkata sama da mutane 30.

Jami'ai sun bayyana yiwuwar samun karin wadanda za su salwanta sakamakon harin, daga dai yadda aka yi nazarin hotunan bidiyo da aka nada a wajen da kuma suka yi ta wadari a shafukan sada zumunta.

Mazauna kewayen yankin da wuraren shakawatar ke a ciki a birnin na Mogadishu dai sun ce sun kwashi lokaci suna ta jin karar harbe-harben da suka hakkake cewa mayaka masu ikirarin jihadi ne ke aikata ta'asar.

Akwai ma tashin nakiyoyi da suka biyo bayan harbe-harben kamar yadda shaidu suka tabbatar.