1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Wuraren tarihin Afirka ba su samun kulawa

August 6, 2021

Ba kasafai Afirka ke samun hankali game da wuraren tarihin duniya da UNESCO. A cewar kwararru sun ce an fi mayar da hankali ne a kan wadanda suke a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/3yetc
Äthiopien Lalibela | Orthodoxe unterirdische monolithische Kirche Bete Giyorgis
Hoto: picture alliance / Sergi Reboredo

A wannan shekara hukumar kula da ilimi da al’adu na Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta yi zamanta na 44, inda aka sanya wuraren Afirka biyu cikin jerin wadanda ta ayyana a matsayin wuraren tarihi na duniya. Wuraren biyu kuwa su ne wani tsohon masallaci a arewacin kasar Ivory Coast da kuma dajin shakatawa na Ivindo da ke kasar Gabon.

Sai dai fa yayin da a wannan zaman Afirka gurabe biyu kacal ta samu, an bai wa Turai sabbin wuraren tahiri 16. Haka ma wasu sauran nahiyoyi su ma sun samu wurare 16 daga cikin wadanda suka shiga gasar zama karkashin hukumar ta UNESCO.

Yamassoukrou, Elfenbeinküste | Moschee | Weltkulturererbe
Hoto: Mehmet Kaman/AA/picture alliance

Sai dai masana harkar tarihi sun bayyanan dalilan da suka sa zaben wuraren tarihin UNESCO fifita bangarorin tarihi da suka shafi Turai. Dalili kuwa shi ne, da farko an mayar da hankali ne bisa manyan coci-coci da ke da dadadden tarihi da wuraren ibada na Hindu hadi da tsoffin wasu muhimman garuruwa. Don haka kasashen da ke da fasahar zamani, su ke iya kare wuraren tarihinsu kuma su ke da karfin tattalin arziki. 

Ita ma dai kanta hukumar kula da wuraren taihi ta Majalisar Dinkin Duniya, ta tabbatar da cewa akwai gyaran da ake bukatar yi game da zaben wuraren tarihi da ake yi a duniya.

Sai dai masana sun bayyana cewa daga cikin matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta da ke hana samar da wuraren tarihi akwai rashin zaman lafiya.

An yi misali da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango wacce ke da dadaddun wuraren tarihi, amma saboda ayyukan ‘yan bindiga ba a iya shiga yankunan balle a ce an samu daukar bayanai da ake bukata.

Irin wannan kuwa shi ne ke faruwa a kasashen Afirka da dama wanda kuma ba karamin kalubale ne a wajen tantance wuraren tarihi ta yadda za a iya sanya su karkashin hukumar ta UNESCO.