'Yan sanda sun afka wa masu goyon bayan adawa a Kwango
December 27, 2023'Yan sanda a Kinsasha babban binin kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun tarwatsa taro na magoya bayan 'yan siyasa inda rahotanni ke tabbar da cewa sun ma raunata mutane da dama, daidai lokacin da 'yan kasar ke dakon sakamakon zaben da aka yi a makon jiya.
Kusoshin jam'iyyun hamayya a zaben na Kwango ne dai suka yi kiran da a fito a yi zanga-zanga, bayan bijire wa zaben da ga dukkan alamu Shugaba Felix Tshisekedi ke kan hanyar lashewa.
Hukumar zaben kasar CENI, ta ce Shugaba Tshisekedin ya samu kaso 79% na kuri'un da aka kada a zaben da aka samu matsaloli na rashin isar kayan aiki da ma hardewar na'urori.
Hankali dai na kasar Jamhuriyar Dimkurdaiyyar Kwango mai fama da fitintinu ciki har da yaki da mayakan tawaye a yanzun.
Har yanzu dai ana ci gaba da dakon sakamakon zaben na Kwango.