1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar da EU na neman ja wa ta’addanci birki a Sahel

Ramatu Garba Baba
May 18, 2023

Bisa taimakon Kungiyar Tarayyar Turai, kwararru a harkar tsaro na kasashe 10 na Sahel da Sahara na duba rawar da fararen hula za su iya takawa a yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4RXee
Kungiyar EU na taimaka wa Nijar yakar ta'addanci
Kungiyar EU na taimaka wa Nijar yakar ta'addanciHoto: Marou Madougou Issa/DW

Bisa taimakon Kungiyar Tarayyar Turai, Kwararru a harkar tsaro na kasashe 10 na Sahel da Sahara na duba rawar da fararen hula za su iya takawa a yaki da ta'addanci baya ga matakan soja da ake dauka don tinkarar matsalar. Kungiyar Tarayyar Turai ce ta dauki nauyin shirya wannan taro a karkashin shirin EUCAP-Sahel mai kula da taimaka wa kasashen Sahel a yaki da ta'addanci.