Jamhuriyar Nijar: Dakile juyin mulki
March 31, 2021Tuni dai wasu masu fafutukar kare dimukuradiyya a Nijar din, suka fara nuna damuwarsu game da wannan yunkuri nakifar da gwamnatin shugaba mai shirin barin gado Mahamadou Issoufou ta hanyar juyin mulki, abin da ka iya mayar da dimukuradiyyar kasar baya. Sun kuma bukaci fadar shugaban kasar da ta gaggauta fito wa ta yi wa al'umma bayanin abin da ya faru.
Karin Bayani: Shekaru 20 bayan kisan Bare Mainassara
Ko da ya ke cewa har gwamnati ba ta fito ta yi bayani ba tukuna, amma wasu rahotanni sun bayyana cewa sojojin rundunar sojan sama da aka fi sani da Escadrille a karkashin jagorancin shugaban wannan runduna suka yi yunkurin juyin mulkin ta hanyar kai farmakin a cikin motocin yaki guda biyar, wadanda suka girke a gabashi da yammacin fadar shugaban kasar, inda daga nan suka dinga barin wuta ga sojojin fadar shugaban kasa da ke kofar farko ta shiga fadar.
Nan take sojojin fadar shugaban kasar suka mayar da martini mai karfi, wanda ya ba su damar dakile harin sojojin ta hanyar kashewa tare da kame wasu daga cikinsu, wadanda ake can yanzu haka ana yi musu tambayoyi a ofishin jami'an tsaron gendarmerie da ke birnin Yamai. Rahotanni sun nunar da cewa, suma a nasu bangaren wasu daga cikin sojojin fadar shugaban kasar sun jikkata.
Karin Bayani: Ci gaba da tsokaci kan yunkurin juyin mulki a Nijar
Bayan afkuwar lamarin dai, shugaban kasa mai barin gado a Jamhuriyar ta Nijar Alhaji Mahamadou Issoufou ya jagoranci bikin kaddamar da sabbin mambobin kotun tsarin mulki da suka maye gurbin wadanda suka yi ritaya da safiyar Laraba. Tashar DW ta samu tattaunawa ta wayar tarho da shugaba mai jiran gado Bazoum Mohamed wanda ya tabbatar da yana cikin koshin lafiya. Wannan yinkurin juyin mulki da ya ci tura dai, ya faru ne kasa da sa'o'i 48 a rantsar da sabon shugaban kasa.