Fargaba kan yunkurin kwace birnin Bakhmut
December 3, 2022Kasashen yamma na baiyana fargaba kan wani sabon yunkurin Rasha na kwace ikon birnin Bakhmut da ke Ukraine, an gano yadda rundunar Rashan ke kokarin ganin ta yi wa birnin kawanya, masana sun ce sun hango barazanar da wannan nasara ka iya jefa wasu yankunan da ke kawayen birnin na Donetsk.
Britaniyya na daga cikin kasashen da ke baiyana damuwa a game da wannan sabon salon yakin da Rasha ta dauko da tuni ya soma shan suka daga kasashen da ke goyon bayan Ukraine a fadan da suke da Mosko.
Shugaba Volodymr Zelensky a na shi bangaren kuwa, kira ya yi, na a rage farashin man Rasha a kasuwannin duniya, yana mai cewa, hakan zai yi matukar tasiri a karya tattalin arzikin kasar da ke mamayar Ukraine.
Rasha dai ita ce kasa ta uku a duniya wajen samar da mai bayan Amirka da Saudiyya, kuma kusan rabin man da ta ke fitarwa na zuwa kasashen Turai.