1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kafa gwamnati a Sudan ta Kudu

September 12, 2019

Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa Shugaba Salva Kiir da madugun tawayen kasar Riek Machar, sun amince da kafa gwamnatin hadaka cikin makonni da ke tafe.

https://p.dw.com/p/3PRuA
Südsudan -  Riek Machar und  Salva Kiir
Hoto: Reuters/M. N. Abdallah

Bayan wata ganawar kwanaki biyu da suka yi a Juba babban birnin kasar ne dai Shugaba Kiir da jagoran na tawaye Riek Machar suka cimma wanna matsaya.

A cewarsu za su kafa gwamnatin ne a ranar 12 ga watan Nuwambar bana, baya ga wasu batutuwan da baki ya zo daya a kansu.

Daga cikin batutuwan dai har da tsarin gudanar da tsaron kasar da batutuwa da suka shafi iyakoki sai kuma adadin jihohin da za su kasance a Sudan ta Kudun a nan gaba.

Kasar wacce ita ce jaririyar kasa yanzu a duniya, an same ta ne a shekara ta 2011.