Kalubalen zaben kananan hukumomi a Najeriya
March 28, 2021Matakin da hukumomin zabe da kuma gamayyar jamia'an tsaro da dukkanin masu ruwa da tsaki suka dauka, na kokarin ganin an rattaba hannun kan wannan yarjejeniya ta zaman lafiya tsakanin wadannan Jam'iyyun siyasa guda 10 da za su shiga zaben, na da nasaba ne da yadda ake son kauce wa tashin hankali da kuma tayar da zaune tsaye dangane da yadda ake tunanin zaben ka iya kayawa.
Dama dai tuni jam'iyyar APC mai adawa a jihar ta ce ba za ta shiga wannan zaben ba, saboda yadda suke ganin tun matakin farko akwai rashin adalchi innji Hon Isah Sadiq Achida shugaban jam'iyyar APC na jihar Sakkwato. To amma kuma a daya bangaren jam'iyyar PDP mai mulki a jihar, ta ce ta shirya tsaf domin tunkarar zaben shugabannin kananan hukumomin da kansiloli.
Karin Bayani:Musulmi da Kiristoci a Jos na siyasa a tare
Duk dai da irin doki da fatan da mutane ke yi ga wannan zaben na kananan hukumomi da aka kwashe dogon lokaci ba a yi ba a jihar ta Sakkwato, wasu na ganin kauracewa shiga zaben da jam'iyyar APC ta yi zai rage armashinsa.