1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zafafa harin Rasha a Ukraine

Usman Shehu Usman
July 20, 2023

Kasar Rasha ta gargadi jiragen ruwan kasashen duniya da su yi nesa da tashoshin jiragen ruwan kasar Ukraine don za a rika daukarsu a matsayin abokan gaba wanda kan sa a iya kai masu farmaki

https://p.dw.com/p/4UCV2
Vostok 2018 military exercise in Transbaikal Territory, Russia
Hoto: Vadim Savitsky/TASS/dpa/picture alliance

Kasar Ukraine ta yi Allah wadai bisa gargadin da Rasha ta yi wa jiragen ruwan kasashen duniya kan yin zirga-zirga izuwa gabar ruwayen Ukaraine. Ukraine na martani ne bisa gargadin da Rasha ta yi cewa nan gaba duk wani jirgin ruwan da aka gani ya nufi Ukraine to ana iya daukar sa a matsayin abokin gaba, ma'ana Rasha na iya kai masa hari. Ma'aikatar harkokin wajen Ukaraine ta yi kakkausar sukar cewa, Rasha a yanzu ta yi shelar hana ko wane jirgin ruwa hatta na farar hula ya zama a bun kaiwa hari. Rasha dai ta kara zafafa matakai kan Ukraine, musamman tun bayan harin da Ukraine ta kai wa gadar da ta hade tsibirin Crimea da kasar Rasha.

Haka zalika kasar Rasha ta zafafa hare-hare kan tashar jiragen ruwan Ukaraine na Odesa. Hukumomin Ukraine sun bayyana cewa farmakin da Rasha ke kaiwa ya lalata wasu kayakin aikin tashoshin jiragen ruwa, kuma Rasha na yin haka ne don lalata tashar. Kasar ta Rasha ta fara zafafa hare-haren sa'o'i bayan ta janye daga yarjejeniyar da aka kulla bayan fara yakin Ukraine, wace ke bada damar fitar da hatsi daga Ukraine izuwa kasuwannin duniya.  Sakatare janar na MDD, tuni ya yi Allah wadai da hare-haren, wadanda ya kira ba abin da za su haifar illa kara dagulewar al'amura a Ukrauine. Rasha dai a cewar Ukraine tana kai hare-haren da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka.