An shiga jimamin sace dalibai a jihar Zamfara
February 26, 2021Ana ci gaba da alhinin sace daliban makarantar sakandaren kwana ta Jangebe da ke karamar hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara da wasu 'yan bindiga suka sace a daren Alhamis din da ta gabata, lamarin dai ya saka al'umma musamman iyayen yara cikin rudani. Gwamnatin Zamfara na daga cikin jihohin da ke yunkurin yin sulhu da 'yan bindigan da ake zargi da hana zaman lafiya a yankin arewacin kasar.
Karin Bayani: Matakin sulhu da 'yan bindiga
Wannna kusan shi ne karan farko da aka shiga makatarantar kwana ta mata, aka kwashi dalibai a shiyyar arewa aaso yamma, lamarin da ya tayar da hankulan al'umma ta la'akari da yadda lamarin ya auku a daidai lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ke cewa tana sasantawa da 'yan bindiga. Sace wadannan dalibai na zuwa ne, a lokacin da gwamnonin arewacin kasar ke taro a jihar Kaduna da zummar magance matsalar tsaron da ta addabi yankin.
Karin Bayani: Daliban Kagara sun fada hannun masu satar mutane
A dade ana kai ruwa rana kan kokarin lalubo hanyar shawo kan matsalar satar mutane da garkuwa da su domin neman kudin fansa, kungiyar gwamnonin Najeriya ta amince da bin hanyar sulhu da masu kai hare-haren a yayin da wasu ke ganin, ba zai taimaka a magance matsalar ba. Wannan sace daliban na zuwa ne, bayan sace daliban sakandaren Kagara na jihar Neja, amma kuma karo na hudu da ake sace dalibai daga makarantun kwana da ke matukar girgiza al'umma a ciki dama wajen Najeriya. Kawo yanzu tun bayan sace 'yan matan makarantar Jangebe, karatun kurma na zaman tunanin mahukuntan tarrayar Najeriyar da har ya zuwa yammacin wannan Juma'a, ba su ce uffan ba kan harin da ya tayar da hankali a cikin kasar. Babu dai tawagar al'adar da kan ziyarci sansanin aikata laifin, sannan kuma babu sanarwa kwantar da hankula daga fada ta gwamnatin kasar. Ana dai kallon Satar 'yan makarantar Jangeben da ke zaman na uku cikin arewacin kasar a kasa da watanni uku a matsayin wani sabon yanayin da ke shirin wucewa da tunanin 'yan mulki na kasar. A cikin watan Disamban da ya shude ma, barayi sun sace wasu 'yan makarantar kwana na Kankara da ke jihar Katsina. A yayin kuma da har yanzu ake gwagwarmayar ceto 'yan makarantar Kagara da aka sace a jihar Neja.