1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Nigeria ta biya kudin fansa ga Boko Haram

Salissou Boukari
August 17, 2018

A Najeriya ana maida martani a kan rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da ya nuna cewa gwamnatin kasar ta biya makudan kudade ga kungiyar Boko Haram a lokacin da ta sako 'yan matan Daptchi a watan Maris

https://p.dw.com/p/33Joc
Nigeria Buhari - Dapchi Mädchen freigelassen
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da 'yan mata 'yan makaranta na garin DapchiHoto: DW/U. Musa

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya karyata matsayin Najeriya wadda tun a watan Maris lokacin da aka sako ‘yan matan na Daptchi ta ce bata biya ko sisin kwabo ba, abinda rahoton na kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniyar ya ce lallai an biya makudan kudadde ga kungiyar ta Boko Haram kafin suka saki 'yan matan na Daptchi. kungiyar dai na amfani da garkuwa ko sace jama'a a matsayin hanyar samun kudi a yankin tafkin Chadi.

Nigeria - Massenentführung Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Tuni dai gwamnatin Najeriyar ta bakin ministan yada labaru da ala'adu Lai Mohammed ta mayar da martani, tana kalubalantar duk mai dagewa kan cewa an biya kudi ya kawo shaida.

"Ya ce mu a garemu nauyi ne a kan batun mutuncinmu shi yasa ko a lokacin gwamnati a karkashin masu shiga tsakani ta tunatar da su yarjejeniyar da aka cima cewa ba za'a kara sace yara ba, shi yasa bamu biya kudi ba kuma ba mu yi wata musayar fursunoni ba, duk wani labarin da ya saba da wannan karya ne."

A yayin da gwamnati ke bayyana cimma yarjejeniyar cewa ba za'a kara samun sace wani ba daga kungiyoyin, masharahanta na bayyana karfafa bin hanyar sulhu don shawo kan lamarin musamman bisa bayanan halin da masu kai hare-haren ke ciki yanzu da suke ganin ya samar da wannan dama.