Najeriya: Zargin Tinubu da fataucin muggan kwayoyi
November 10, 2022Yamadidin da ake yi na wannan zargi da aka yi wa dan takarar neman shugabancin Najeriyar a karkashin jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu tare da kama shi da laifi, na tayar da kura a fagen siyasar Najeriyar. Takardu ne dai da ke dauke da hatumin kotun kasar Amirka da ya tabbatar da tuhumar da aka yi wa Tinubu a shari'ar da aka yi a 1993, sai dai kakakin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar APC, Festus Keyamo ya ce akwai bukatar fahimtar lamarin. A cewarsa Tinubu ba ya cikin wadanda aka kai kara a wannan shari'ar kuma idan aka duba takardar ba a ambaci Tinubu ba, lambar asusun banki ne kadai aka ambata aka ce tasa ce dan haka babu chaji kuma babu inda aka same shi da laifi.
Tuni dai muhawara ta kaure a fagen siyasar Najeriyar, saboda sake bayyanar wadannan takardu da ma abin da wannan ke nunawa a fagen shari'a. A yayin da ake ci gaba da cece-kuce a kan wannan lamari, jam'iyyar APC ta ce, sake bayyana takaradun zargin ya makaro. Tuni dai kungiyoyin yaki da cin-hanci da rashawa a Najeriyar suka bayyana cewa, zargi na tu'ammali da miyagun kwayoyi babban al'amari ne da bai kamata a yi wasa da shi ba. Zargi ne koma dai yarfe ne na 'yan siyasa ya rage ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na Najeriyar musamman ICPC da EFCC, domin Amirka ta dade da kammala nata aiki a kan wannan laifi tun a shekara ta 1993.